Mai da jama’a a gaban komai ita ce ƙa’idar gwamnatin ƙasar Sin

Daga MINA

Abokai, yau na zana wani layin dogo da ake kira “Layin dogo na Qinghai-Tibet” wanda ya hada birnin Xining na lardin Qinghai da birnin Lhasa na yankin Tibet.

An shimfida layin ne a tudun dake da matsakaicin tsayi mita 4000 daga leburin teku, hakan ya sa ya zama layin dogo mafi tsayi a duniya.

Tudun Qinghai-Tibet na da nisa matuka da teku, saboda matuƙar tsayi, aikin shimfida layin dogo ko hanya a wurin, na fuskantar matuƙar wahala.

Ya zuwa shekarar 1949, hanyar mota mai tsawon kimanin mita 1000 ne kawai yankin ke da su, baya ga kuma kwale-kwale da kuma layin jigila mai kama da lilu aka yi amfani da su. A cikin shekaru da dama da suka gabata, saboda ƙarancin hanyoyi da layin dogo, yankin ya fuskanci koma gaba matuƙa.

Shahararren mai yawon shaƙatawa ta jirgin kasa dan ƙasar Amurka Paul Theroux ya rubuta a cikin littafinsa cewa, “Ba zai yiwu a shimfida layin dogo zuwa Lahsa ba saboda tsaunin Kunlun yana da tsayi.”

Amma duk da mawuyacin hali na wannan yanki, gwamnatin Sin ta lashi takobin gina layin dogo don amfanawa jama’ar dake kan wannan tudu.

Daga shekarar 1958 zuwa 2006, gwamnatin Sin ta daidaita ƙalubalolin da aka fuskanta wajen gina layin dogon sakamakon duwatsu masu tsayi da daskarewar ƙasa da kare muhalli da sauransu, inda ta shafe shekaru 48 tana aikin gina layin dogo na Qinghai-Tibet, mai tsawo kilomita 1956 dake da tasoshi 85.

Ya zuwa ƙarshen watan Yuni na bana, an yi jigilar fasinjoji kimanin miliyan 260 ta wannan layi, daga cikinsu masu yawon shakatawa dake shiga ko fito yankin Tibet ya kai fiye da miliyan 31.

Ban da wannan kuma, a watan Yuli na bana, an fara aikin inganta tashar Delingha, matakin da ya daga matsayin mu’amula tsakanin yankin da sauran sassan ƙasar da ma kyautata zaman rayuwar jama’ar wurin.

Jama’ar ƙabilar Zang sun yaba wa wannan layin dogo, ta hanyar rera wata waka cewa, “Muna matuƙar maraba da wannan layin, wanda ya haɗa mu da sauran wurare. Wannan layi mai muhimmanci ya samar da zaman rayuwa mai kyau da alheri da wadata……”

Layin dogo na Qinghai-Tibet na da babbar ma’ana wajen kawar da talauci a yankin Tibet da ingiza mu’ammala tsakanin ƙabilu daban-daban na ƙasar da tabbatar da samun wadata tare a tsakaninsu, da ma ingiza bunƙasuwar tattalin arziki da bunkasuwar al’ummar lardin Qinghai da jihar Tibet.

Shimfida layin dogo a wannan yanki, wanda a baya wasu ke ganin ba zai taɓa yiwuwa ba, a halin yanzu gwamnatin Sin ta yi nasarar kammala shi.

Aikin da ya zama abin mamaki a tarihin gina layin dogo a duniya, kuma ya bayyana manufar gwamnatin Sin ta bauta wa jama’a da mai da jama’a a gaban kome.

Mai zane da rubuta: MINA