Ya kamata Amurka ta soke takunkumi idan tana son taimakawa Afirka

Daga CMG HAUSA

Ranar 25 ga wata, rana ce ta yaƙi da takunkumi, wadda ƙungiyar SADC ta ayyana. Wasu ƙasashen Afirka sun sake yin kira ga Amurka da sauran ƙasashen yammacin duniya da su soke takunkumin da suke ƙaƙaba wa ƙasar Zimbabwe.

Amurka ta ɗauki sama da shekaru 20 da sanyawa Zimbabwe takunkumi ya zuwa yanzu. Alkaluman ƙididdiga sun nuna cewa, Zimbabwe ta yi asarar dalar Amurka fiye da biliyan 40 sakamakon takunkumin da aka sanya mata baki ɗaya. Hakika dai yadda Amurka ta ƙaƙaba wa Zimbabwe takunkumi, ta nuna yadda ta daɗe tana tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasashen Afirka.

A watan Agustan bana, Antony Blinken, sakataren harkokin wajen Amurka ya ziyarci Afirka karo na 2, inda ya gabatar da sabbin tsare-tsaren Amurka kan yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Amurka ta yi shelar cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, za ta ƙara azama kan yadda Afirka take buɗe ƙofa ga ƙetare, da taimakawa Afirka wajen tinkarar annobar cutar COVID-19 da farfaɗo da tattalin arzikin Afirka.

Amma akasarin ra’ayoyin jama’a na ganin cewa, a maimakon taimakawa ci gaban Afirka, Amurka ta yi amfani da Afirka domin samun moriya bisa manyan tsare-tsare, da sunan wai haɗa kai da Afirka.

Yanzu haka sakamakon tsanantar rikicin Ukraine, ya haifar da ƙaruwar barazanar ƙarancin abinci da makamashi, lamarin da ya kawo wa ƙasashen Afirka waɗanda ke neman farfado da tattalin arzikinsu babban ƙalubale.

Duk da haka Amurka da sauran ƙasashen yammacin duniya sun kau da kai daga matsalar da Afirka ke fuskanta wajen samun ci gaba, sun ci gaba da ƙara sanya takunkumi kan ƙasashe masu ruwa da tsaki, har ma sun tilasta wa ƙasashen Afirka ba su goyon baya.

Ko Amurka tana son taimakawa Afirka, ko kuma ba za ta cika alƙawarinta kamar yadda ta yi a baya? Gaskiya ba ta buya. Kafin Amurka ta haɗa kai da Afirka, ya kamata ta soke takunkumin da take ƙaƙaba wa wasu ƙasashen nahiyar.

Mai fassara: Tasallah Yuan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *