Cibiyar horas da malaman makaranta ta NTI ta samu izinin ba da shaidar digiri

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwalejin Horas da Malaman Makaranta (NTI) ta samu izinin ba da shaidar digiri a fannin koyo da koyarwa na ilimi-daga-nesa kamar yadda darakta-janar Farfesa Musa Garba-Maitafsir, mai barin gado, ya bayyana.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ta rawaito a ranar Litinin a Kaduna a yayin da yake miƙa ragamar jagorancin kwalejin ga mai maye gurbinsa, Farfesa Sa’adiyya Sani-Daura.

Garba-Maitafsir ya ce, shugabar na karɓar shugabanci ne a lokacin da komai ya daidaita idan aka kwatanta da lokacin da ya karɓi jagorancin kwalejin.

Ya ce ya karɓi kwalejin ne a lokaci mai wahala, amma ya yi duk mai yuwuwa domin inganta sha’anin karatu, musamman abin da ya shafi duba jarrabawar ɗalibai da sauran al’amura na karatu.

Sannan ya ce ya gaji bashi mai tarin yawa da ya kai Naira biliyan 1.2 a lokacin da ya karɓi shugabancinta, amma ya yi ƙoƙarin biyan kusan sama da kashi 95 na bashin da ake bin kwalejin.

Garba-Maitafsir ya ce, “a lokacina, na yi ƙoƙarin rage kashe-kashen kuɗi ba gaira ba dalili da gyara ɗakin taro da sashen ɗab’in inda ake buga takardun da ake amfani da su a kwalejin.

Shugaban ya ce a tattaunawar da aka yi ta ministoci, kwalejin NTI ta ciri tuta a matsayin mafi hazaƙa a dukkan kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya.

Daga nan ya shawarci shugabar mai jiran gado da ta cigaba da kula da wannan nasara da kwalejin ta samu inda ya yi alƙawarin taimaka mata da gogewar da ya samu da shawara domin kai wa ga gaci.

A yayin da take magana, sabuwar shugabar kwalejin ta NTI kuma mace ta farko da ta zama shugabar, wadda ta ce gwamnatinta za ta ɗora wajen cimma manufofin da aka gina kwalejin a kai da kuma ɗorawa daga inda tsohon shugaban ya tsaya.

Sannan ta buƙaci ma’aikatan su cigaba da aiki tuƙuru da haɗin kai inda ta buƙaci goyon bayan dukkan ma’aikatan hukumar.

Hakazalika ta yi alƙawarin duba dukkan matsalolin da kwalejin ke fuskanta da kuma ƙoƙarin magance su.

Sannan Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya ce shugaba mai barin gado ya kuma zaga da mai jiran gado zuwa wuraren wasu ayyuka da ake kan yi tare da miƙa mata su a wani ɓangare na yin bankwana da kwalejin.

By ukarofi