Cibiyata ta inganta rayuwar jama’a za ta tallafa wa ‘yan Nijeriya – Oluremi Tinubu

Daga IRAHEEM HAMZA MUHAMMAD

Cibiyar Inganta Rayuwar Jama’a, wacce a Turance ake kira da suna ‘Renewed Hope Initiative’ (RHI) ta ƙuduri aniyar rage ƙuncin rayuwa ga al’ummar Nijeriya.

Ta faɗi haka ne bayan taron hukumar gudanarwa ta cibiyar da aka gudanar a ofishinta dake cikin Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock dake Abuja.

Wannan sanarwa ta biyo bayan sanarwa da kakakinta Busola Kukoyi ta fitar.

Uwargidan Shugaban Ƙasa Ahmed Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu wacce ita ce Shugabar cibiyar don inganta rayuwar jama’a ta ce, an kammala tsari domin ƙaddamar da shirin a jihohi 36 da babban birnin Tarayya, Abuja.

Ta furta cewa za a sanya matan gwamnoni da na shugabannin ƙananan hukumomi a cikin shirin.

Sanata Oluremi Tinubu ta ƙara da cewa, ana son tabbatar da ganin waɗanda za su ci moriyar shirin an yi musu rajista da tantance su domin su ci moriyar shirin don samun tallafi da fita daga ƙuncin talauci.

Bugu da qari, ta ce za a fara raba tallafin ne daga ragowar kuɗin da ya yi saura daga kuɗin kamfen ɗin 2023 kafin a nemo tallafi daga ‘yan kasuwa da hukumomi da cibiyoyi masu bada tallafi na duniya.

Sanata Oluremi Tinubu ta ce, “shirin zai ba da damar a tallafawa talakawa, don su ci ribar romon mulkin dimokuraɗiyya muraran.”

Uwargida Oluremi Tinubu za ta yi taro da matan gwamnoni ran 14 ga wannan wata na Yuli domin tsara yadda shirin zai kai ga cin nasara gadan-gadan.

Taron ya sami halartar Mataimakiyar Shugabar Cibiyar kuma Uwargidar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Kashim Shettima; da Sakatariya kuma Uwargidar Gwamnan jihar Imo, Misis Chioma Uzodinma, da Uwargidar Shugabar Majalisar Dattijai, Unoma Akpabio; da Uwargidar Shugaban Ma’aikata a ofishin Shugaban Ƙasa, Salamotu Gbajabiamila; da Shugabar Mata ta Jamiyyar APC, Dr Betta Edu da Kuma Farfesa Hafsat Ganduje waɗanda sune jagororin cibiyar.