Kwararar Hamada: Gwanatin Tarayya ta dasa itatuwa sama da miliyan 10 a jihohi 11

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

A ci gaba da ƙoƙarin da take yi na magance matsalar kwararowar hamada da ke addabar wasu jihohin ƙasar nan, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Matsalar Hamada ta Ƙasa ta dasa itatuwa sama da miliyan 10 a jihohi 11 faɗin Nijeriya.

Darakta Janar na Hukumar Kula da Kwararar Hamada, (NAGGW), Dokta Yusuf Maina Bukar ne ya bayyana haka a bikin zagayowar dashen itatuwa na shekarar 2023 a Gusau, babban birnin jihar ranar Alhamis.

Dokta Bukar wanda ya samu wakilcin Daraktan Gudanarwa na hukumar, Nasiru Ismail, ya bayyana cewa, jahohi 11 da kwararar hamada ta shafa su ne: Sakkwato, Kebbi, Katsina, Zamfara, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Yobe, Borno da kuma Adamawa. .

“Hukumar National Agency for the Great Green Wall (NAGGW) hukuma ce wadda Gwanatin Tarayya a ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, wacce aka kafa don magance matsalar gurɓacewar ƙasa da kwararowar hamada da bunƙasa samar da abinci da tallafa wa al’umma domin su dace da sauyin yanayi.” Inji shi.

A cewarsa, hukumar NAGGW ita ce cibiyar da Nijeriya ta mayar da hankali wajen ganin an cimma manufar Ƙungiyar Tarayyar Afirka don sauya yanayin sahara da kuma yankin sahel.

Ya kuma yi nuni da cewa, hukumar ta sanya ranar 13 ga watan Yuni na kowace shekara domin gudanar da bikin yaƙi da kwararar hamada a ƙasar nan.

A cewarsa, hukumar ta zabo wasu muhimman wurare a Jihar Zamfara domin ƙaddamar da dashen bishiyoyi da suka haɗa da makarantu, sakatariyar jihar, gidan gwamnati da dai sauransu.

Dokta Bukar ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da ta kula da itatuwan da aka dasa domin cimma burin da ake buƙata.

Da yake jawabi tun da farko, Gwamnan Jihar Zamfara, Dokta Dauda Lawal, ya yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar domin magance matsalar kwararowar hamada da ya addabi wasu sassan jihar.

Gwamna Dauda wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren Ma’aikatar Muhalli ta Jihar, Muhammad Abubakar, ya ce, gwamnatinsa za ta yi dukkan ƙoƙarin da ya dace ta hanyar kula da itatuwan da hukumar ta daddasa a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *