Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Wata Babbar kotu ta hana Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Kabir Yusuf ci gaba da shirin rusa gidaje da ke kan titin BUK a Ƙaramar Hukumar Gwale ta jihar.
Kotun ta amince da buƙatar da aka gabatar mata a ranar 4 ga watan Yuli, wanda Ibrahim Adamu, Lauyan masu ƙara a madadin Malam Bashir Abdullahi da wasu mutum 19 suka gabatar.
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Gwamna Abba Yusuf da babban lauyan gwamnati da kuma ofishin kula da filaye da tsare-tsare da raya biranen na Jihar Kano.
Tuni dai Mai Shari’a Hafsat Yahaya-Sani, ta bayar da umarnin wucin-gadi na hana waɗanda ake ƙaran, ko wakilan su, ko ma’aikatan su ko kuma masu yi wa jihar aiki shiga filin har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukuncin a kai.
Daga bisani dai Alƙalin ta ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har zuwa ranar 26 ga Oktoba mai zuwa.