Cin kifi mai guba ya yi sanadin mutuwar almajirai huɗu a Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Almajirai huɗu sun rasu a Jihar Kano bayan sun kamu da matsananciyar rashin lafiya sakamakon cin wani kifi da ake zargin ya gurɓata, yayin da wani ɗalibi ya tsira bayan ya dakatar da cin kifin tun kafin ya kammala.

Mamatan sun haɗa da Abdulfatah Mohammed, mai shekaru 15; Yusuf Nuhu, 16; Buhari Iliyasu, 14; da Ibrahim Muhammad, mai shekaru 22.

Dalibi na biyar, Auwalu Surajo, mai shekaru 18, ya tsira bayan ya ƙi ci gaba da cin kifin, kuma a halin yanzu yana karɓar magani.

Daliban suna karatu a wata makarantar Tsangaya ta koyar da Alƙur’ani mallakin Gwani Malam Iliyasu Mai Tsangaya, da ke Kadage Sharifai, ƙaramar Hukumar Ungogo a Kano.

Surajo Unguwar Gareji, wani abokin ɗaya daga cikin mamatan, ya bayyana cewa ɗaliban sun fara cin kifin da misalin ƙarfe 7:00 na safe, bayan ɗaya daga cikinsu ya fito da shi.

Ya ce, ya ɗanɗana kifin, amma nan take ya daina ci saboda ya lura da cewa ɗanɗanonsa ba kamar yadda kifi mai lafiya yake ba.

“Na ɗanɗana kifin, amma nan take na daina ci saboda ɗanɗanonsa bai yi daidai ba.”

Wani ɗalibi, Malam Umar, shi ma ya ce ya ƙi cin kifin bayan ya fara zargin cewa akwai matsala.

A cewarsa, jim kaɗan bayan sauran ɗaliban sun ci kifin, huɗu daga cikinsu suka suma tare da fara nuna alamomin rashin lafiya mai tsanani. Ya ce nan take aka sanar da malaminsu, wanda ya shirya kai ɗaliban asibiti.

Sai dai, a cewarsa, likitoci a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano daga baya sun tabbatar da mutuwar ɗaliban huɗu.

Tun da farko, Shugaban Tsangaya Media Network, Gwani Sani Musa Nuhu, ya tabbatar da cewa an garzaya da ɗaliban zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano bayan sun kamu da rashin lafiya sakamakon cin abincin da ake zargin ya gurɓata.

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce ɗaliban huɗu sun mutu a asibitin a daren Lahadi, 16 ga Agusta. Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne a gidan Malam Iliyasu Zulyadaini, inda Abdulfatah yake gudanar da wasu ayyukan gida.

Wani mazaunin yankin, Malam Aliyu, ya ce Abdulfatah kan share ɗakuna da harabar gidan, kuma ana zargin ya gano kifin ne ƙarƙashin wata kujera yayin da yake aikin share-share.

A cewarsa, yaron ya ɗauki kifin zuwa waje ya raba shi da sauran abokansa, ba tare da sanin cewa mai yiwuwa kifin ya gurɓata ba.

Aliyu ya ce, sai bayan an kai ɗaliban asibiti ne ya samu labarin abin da ya faru, yayin da fahimtar ainihin abin da suka ci ta ɗauki ɗan lokaci.

Daga bisani aka yi jana’izar gawarwakin ɗaliban huɗu bisa tsarin addinin Musulunci, bayan samun izini daga Dagacin yankin da kuma ‘yan sanda.

Mai makarantar Tsangayar, Gwani Malam Iliyasu, ya bayyana mutuwar ɗaliban a matsayin babban bala’i da ya girgiza iyalansu da al’ummar makarantar.

Ya ce ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu ɗansa ne, yayin da wani kuma ɗan ɗan uwansa ne. Sauran biyun kuwa, a cewarsa, ’ya’yan abokansa ne.

Iliyasu, wanda asalinsa ɗan Jihar Jigawa ne, ya ce ya kafa makarantar Alƙur’ani ne shekaru da dama da suka gabata domin koyar da ɗalibai da kuma taimaka musu wajen haddar Alƙur’ani Mai Girma.

Ya ce da dama daga cikin ɗaliban ’yan garinsu ne, wasu kuma ’yan uwansa ne, abin da ya ƙara masa radadin wannan rashi. A cewarsa, mazauna yankin ne suka sanar da shi jim kaɗan bayan ɗaliban suka fara rashin lafiya.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fara bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar ɗaliban.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce marigayin ’yan asalin ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar ta Jihar Jigawa ne, waɗanda suka je Kano domin karatun Alƙur’ani da haddarsa.

Ya ce rundunar za ta sanar da jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala shi. Likita ya yi gargaɗi kan amfani da magungunan gargajiya ba tare da shawarar ƙwararru ba

Wani likita a Kano, Dr Usman Abdullahi Nagogo, ya bayyana gubar abinci a matsayin rashin lafiya da ke faruwa bayan mutum ya ci abinci ko ya sha ruwa da ƙwayoyin cuta, ƙwayoyin halitta masu lahani ko guba suka gurɓata.

Ya ce alamomin da aka fi gani sun haɗa da tashin zuciya, amai, gudawa, ciwon ciki, zazzaɓi da kasala. A cewarsa, alamomin na iya bayyana cikin mintuna ko sa’o’i bayan cin abincin da ya gurɓata, ko kuma su ɗauki kwanaki kafin su bayyana.

Nagogo ya ce kai mara lafiya asibiti cikin gaggawa na ƙara damar tsira. Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji ƙoƙarin bai wa wanda ake zargin ya ci guba magungunan gida ko wani abu da ba a tabbatar da ingancinsa ba.

Ya shawarci duk wanda ake zargin ya ci abinci mai guba ko ya taɓa wani abu da ba a san asalinsa ba da ya garzaya asibiti domin samun kulawar likita cikin gaggawa.

By ukarofi

Leave a Reply