Cinikayyar waje na Ƙasar Sin ya ƙaru da kaso 9.9 A watan Janairu zuwa Satumba

Daga CMG HAUSA

Alƙaluman hukuma na nuna cewa, cinikayyar kayayyaki na ƙetare na ƙasar Sin, a cikin watanni 9 na farkon shekarar 2022 da muke ciki, ya ƙaru da kashi 9.9 cikin 100, zuwa kuɗin Sin RMB Yuan triliyan 31.11, kwatankwacin Dalar Amurka triliyan 4.75.

A cewar babbar hukumar kwastan ta ƙasar Sin, darajar kayayyakin da ƙasar Sin take fitarwa zuwa ƙetare, ta ƙaru da kashi 13.8 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 17.67, yayin da darajar kayayyakin da ake shigo da su cikin ƙasar daga ƙetare, ta ƙaru da kashi 5.2 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 13.44.

Daga watan Janairu zuwa Satumba, cinikayyar ƙasar Sin da ƙungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da ƙungiyar tarayyar Turai wato EU, da ƙasar Amurka, ta karu da kashi 15.2 cikin 100, da kashi 9 cikin 100 da kuma kashi 8 cikin 100 bi da bi.

A cikin wannan wa’adi, cinikayyar ƙasar Sin da ƙasashen dake aiwatar da shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, ya karu da kashi 20.7 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 10.04.

Mai fassara: Ibrahim