Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS

Ci gaba daga makon jiya

TAMBAYA:

Mummyna Aysha Asas sannu da aiki. Ya kike. Fatan kina cikin jin daɗi. Na kira layinki ya fi a ƙirga don sanar da ke tawa damuwa sai dai ba a ɗauka ba. Ni dai shekarata 17, kuma dan Allah kar ki yi mun mummunar fahimta. Wallahi tun last year mahaifiyar best friend ɗita ta neme ni don mu yi les, kuma ta ja ra’ayina har sai da na amince da ita. tun daga nan ta ke zuwa tana ɗauka ta duk lokacin da babu karatu, ko mu je hotel ko ta kai ni wani gida. To matsalata dai Ina jin tsoron friend ta san abinda mu ke yi. Don yanzu har gidanta ta ke zuwa da ni. Ina neman shawarar yadda zan daina don Allah Ina son friend ɗita, na san rasa abotamu duk ranar da ta san abinda na ke yi da mahaifiyarta. Don Allah mummyna ki ba ni shawara.

AMSA:

Yana da kyau mu yi wa ‘ya’yanmu hukunci daidai da yanayi da hallitarsu. Masu iya magana na cewa, wai “ɗaurowa ta ke a ɗaure alƙali”. Idan kin lura da irin hallitar da ɗanki ko ‘yarki ke da ita ta ɓangaren sha’awa, ki daure ki yi masu hukunci daidai da ita. yawaitar sha’awar yaronki za ta sa ki karya tsarin da kika yi masa na rayuwa don kuvutar da shi daga hallaka. Kuma yin hakan ba zai hana ki ɗora shi kan tsarin bayan kin samar masa nutsuwa.

A wannan zamani ‘yan mata da samari da yawa suna ajiye kunya su sanar da iyayensu aure suke so ayi masu, amma sai iyayen su kawar da kai daga hakan, kuma fa ba sa so su janyo mu su abin kunya, musamman ga ‘ya mace.

Ta yaya kike tsammanin yarinyar da ta ajiye kunya ta sanar da ke irin sha’awar da ta ke da ga aure zata iya riqe kanta tsayin shekarun da kika ɗibar mata na kammala karatu?

Sha’awa na ɗaya daga cikin ababen da masana halittar ɗan adam suka tabbatar na taɓa wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke da alaƙa da fahimta ko ajiyar abu, kamar karatu. Wannan kawai zai iya hana yara mayar da hankali kan karatun da kuka tura su yi a makaranta.

Don haka idan kuna da halin yi wa ‘ya’yanku maza aure, ku daure ko yi masu, daga baya su koma kan karatu ko sana’ar da zata kula masu da gidansu. Idan kuwa babu, ku koya masu hanyar nema, su nemo, su kawo, ku shige masu gaba kan aura masu matan da suka dace.

Kuma abin da ba ku sani ba, shiryayyu daga cikin ‘ya’ya ne kawai ke damuwa da sai kun yi masu aure, saboda a wannan zamani akwai hanyoyi da dama da yara komai ganin da kuke masu a matsayin yara za su samu yadda za su yi shashanci.

Misali ƙarami idan kana shawagi a kafar Facebook kawai za ka ci karo da shashanci da hanyoyin haɗuwa don gudanar da alfasha ba adadi. Akwai wata yarinya da ta tabbar min akwai wani group da ake masu tayin yadda ƙananin yara za su samu damar yin mu’amala.

Idan kana da ƙarancin shekaru kuma kana son ka yi, za ka turo da dubu ɗaya kacal, shi wannan sheɗanin ne zai samar ma abokiyar mu’amala a cikin yara ƙanana mata ko manya da ke da sha’awar lalata ‘ya’yan wasu. Shi ne zai samar ma ku wurin da za ku haɗu idan kana cikin arewacin Nijeriya, (idan ƙananin yara ne. idan kuwa da manya zai haɗa ku zai shirya wa mace har irin ƙaryar da za ta yi ta fita idan akwai tsauri a gidansu).

Karatu bai hana aure, kuma aure bai hana karatu, don haka ku yi abin da ya dace don sauke haƙƙin ‘ya’yan da aka ba ku kiyon su.
Abu na gaba, idan na fahimce ki kina son hanyar da za ki bi don nisanatar wannan ɓarnar.

To hanyar tuba na da sauƙi kuma tana da wahala, sauƙinta idan har a ranmu mu na son tuban, hakan zai sa mu ƙyamaci abin da muke aikatawa da ba daidai ba. Shawarata gare ki tana da matakai; da farko ki sanar da ita ba ki da ra’ayin ci gaba da wannan mu’amala, ki guje amsa kiranta idan ta buƙaci haɗuwarku, idan ta matsanta ki yi barazanar sanar da ‘yarta abin da kuke yi.

Idan duk ba su yi aiki ba, to hanya ta ƙarshe ita ce, sanar da iyayenki su shiga tsakaninki da ita, ba zan ce dole sai kin yi hakan ba, saboda ban san yanayin na ki iyayen ba, amma sau da yawa iyaye na nasarar raba ‘ya’yansu da waɗanda ke cin zarafinsu ta kowacce irin fuska kuma ba tare da sun tona asirinsu ba saboda kasancewarsu ‘ya’yansu.

Ba na jin waɗannan hanyoyin za su kasa bayar da sakamako wanda ake buƙata, sai dai idan har na ƙarshen zai yi ma ki wahala, wataƙila saboda irin iyayen da kike da su, to akwai wasu amintattun malamai da mu ka fara ƙulla alaƙa da su a wasu jihohi na Arewacin ƙasar nan, duk da zuwa yanzu ba su da yawa, Sakkwato, Kano, Kaduna, Abuja, Jos da kuma Nasarawa.

Mu na amfani da waɗannan malaman a sha’ani na rikicin aure ko na iyaye da ke buƙatar dole sai an shiga tsakani fuska da fuska, ko karɓar Musulunci da sauran matsalolin da ke buƙatar ido da ido. To idan kina daga cikin garurun da mu ka lissafo, zai iya zama hanyar da za ki iya bi, domin za su iya shiga a lamarin har kuma ta kai ga su da kansu su neme ta, hakan zai iya kawo ƙarshen lamarin.

Ku aiko da tambayoyinku ta [email protected] ko [email protected]