Yadda za a kawar da tabon fata (1)

Daga AISHA ASAS

Me ake nufi da tabon fata?

Da farko dai za mu soma da bayani kan ma’ana ta tabon fata, kafin mu tsunduma cikin darasin namu.

Tabon fata a ma’anar da muka ba shi shine, wani baƙi da ke dasuwa a wani muhalli na fata da ke fitar da duhu fiye da na asalin kalar fatar jiki, hakan kan faru ne ta sanadiyyar warkewa daga ƙuraje ko wani ciwo da ya samu fata.

Wannan bayyani hakan yake ga fahimta irin tamu, sai dai me hakan yake nufi ko kuma ya wannan baƙin yake samuwa shine ba mu sani ba.

Kamar yadda masana suka ce, tabon fata na samuwa ta sanadiyyar haɗin kai tsakanin ƙwayoyin hallita da ke aiki a ɓangaren fata don samar wa fata kariya daga wata matsala da ke tunkaro ta, hakan zai sa su haɗe kai wurin samar da sinadarin melanin mai yawa don bada kariya ga fatar.

Kamar yadda muka taɓa faɗa a wani darasi namu a baya, shi sinadarin melanin sinadari ne da ke fita a matsirar gashin jikin ɗan adam, walau a jiki ko fuska ko kuma girar ido. Kuma wannan sinadari yana bayar da kariya ga fata tun daga fitar gashin da kuma kare fata daga hasken rana.

Rashin wannan sinadarin zai iya barin fata babu kariya, kamar barin ta a bushe ko tamura, kuma rashin sa ne ke kawo furfura a gashin kai, wanda tsufa na ɗaya daga cikin dalilin da ke rage samuwar wannan sinadarin.

Shi wannan sinadarin na tasiri ga gashi ne sanadariyar kalar da yake fitarwa da ke haifar da baƙin kala a duk inda ya sauka. Wannan dalilin ne ya sa idan ya yawaita a wani wurin yake haifar da baƙi fiye da sauran wurare.

A taƙaice yawan fitar wannan sinadarin yawan duhun da fatar zata yi.

A lokacin da fata ta ke fuskantar barazana ta hasken rana ko ƙwayoyin cuta da ke zama ƙuraje ko makamantan su, ƙwayoyin hallitar da ke haifar da wannan sinadarin za su yi hanzarin sakinsa da yawa don samun saƙon neman agaji da suka yi daga fata, wannan ne zai sa ko da ƙurji zai mutuwa ko wani ciwo, kamar yankuwa ko ƙuna da sauran su, ko wurin ya warke zai bar duhu wanda shine muke cewa tabon fata.

Idan mun fahimci bayyanin, kenan tabon fata na da alaƙa da wannan sinadarin, wannan zai tabbatar mana tabon fata karan kansa ba ciwo ba ne.