ICPC ta rufe jami’o’i 68 na bogi a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar da ke yaƙi da almundahana da sauran lafukan da suka shafi cin hanci ta ICPC a Nijeriya, ta ce, ta rufe jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha da ke bayar da shaidar digiri na bogi 62 a faɗin ƙasar.

Hukumar ta ce, wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a Nijeriya, domin kuwa babu wata jiha a faɗin ƙasar da ba a samu irin wannan makarantu ba a cikinta.

Cikin shekaru da ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a ɓoye, ta kai ga gano adadin makarantu da suka haɗa da jami’o’i da kwaleji-kwaleji 62 na bogi da ke bayar da shaidar digiri a faɗin Nijeriya.

Amma ta ce, an fi samun irin waɗannan makarantu a Arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Hukumar ICPC ta ce, ta bayyana wannan gagagrumar ɓarna ne, domin shaida wa ‘yan Nijeriya cewa tana kallon duk wani mai shirin yin al-mundahana a kowanne fanni.

Ta ƙara da cewa, ko da za a ɗauke kai a ko ina, to ba dai a ɓangaren ilimi ba, domin kuwa duk ƙasar da ba ta da tsarin ilimi ingantacce, to gobenta za ta iya kasancewa cikin ƙila wa ƙala.

Muhammad Ashiru Baba shi ne shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar ICPC, ya kuma ce abin takaici ne halin da ilimi ya tsinci kansa a Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, “mafi yawan Jami’o’in ba su da ginin kansu, a maimakon haka suna amfani da gine-ginen Sakandire da na Furamaren da ba a karatu a ƙarshen mako domin gudanar da karatunsu, kuma cikin shekara guda mutum zai samu shaidarsa”.

Wanda hakan ke nufin iyayen da suke kai yaransu irin waɗannan wurare, sun kwana da sanin inda suke kai yaran nasu ba wajen kwarai ba ne.

Ashiru Baba ya ce, a kwanakin baya har kama sansanin ‘yan bautar ƙasa suka yi na boge, wani abu da suka jima yana ɗaure musu kai.

ICPC ta cimma nasarar kulle waɗannan jami’o’i ne ta hanyar bayanai da ta samu daga hukumar da ke kula da Jami’o’i ta Nijeriya NUC, kuma tun daga 2016 ta ke gudanar da wannan aiki har ya zuwa yau.