Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Kimanin mutane sama da 450 anbaliyar ruwan sama ta rabasu da mahallinsu a ƙaramar hukumar Miga da ke Jihar Jigawa
Jawabin hakan ya fito ne daga bakin jami,in hukumar bada agajin gaggawa SEMA na Jigawa. Malam Musa Mada Jahun ya sanar da wakilinmu haka a wata zantawa da ya yi dashi a hedikwatar ƙaramar hukumar dake Miga
Yace waɗanda ta,adin ruwan saman ya raba da gidajensu yanzu haka suna samun mafaka ne a makarantu da asibitoci da kuma wasu gine-ginen gwamnati ƙaramar hukumar ta na ba su kula.
A bayaninsa ya ce wuraren da ‘yan gudun hijira su ke zaune ya haɗa da ƙauyen Tsakuwawa,Nasarawa,koya,Hantsu da Kuma ƙauyen Sara Wuya.
Ya kuma nuna takaicinsa akan yadda wata mata mai ciwon mama ta sami kanta a ciki na halin larurar rashin lafiya da take fama Kuma gashi ta na shayar da ƙaramin jariri wanda bai wuce ‘yan watanni da haihuwa ba .
Ya ce matar ga alamu tana cikin damuwa saboda ba ta da halin da za ta baiwa jaririn kulawar da ya ke buƙata kasancewar maman na ta biyu sun harbu da ciwon daji.
Matar mai suna Ruƙayya Sale da ta ke bayani tace ta kamu da wannan ciwo na mama kimanin wata biyu baya.
Lamarin ya sa gaba ɗaya ƙarfinta ya Ƙare ba ta iya shayar da jaririn na ta domin duk abin da ta mallaka ya Ƙare wajen neman magani a asibiti.
Ya ci gaba da cewa mijinta malam sale mai ƙaramin ƙarfi ne da kyar ya ke iya samo masu abinci saboda wanki ya keyi da guga ala tilas suka daina zuwa asibiti su ka koma amfani da maganin gargajiya .
Saboda hakane take neman taimakon jama’a wajen bata agaji da kuɗi ko magani da zai rabata da ciwon ko Kuma abincin jarirai dan ganin an ceto lafiyar jaririn na ta.
Yaci gaba da cewar yaron na ta wanda aƙalla zai wata shida a duniya bayan haifar shi da wata biyu ne ta sami wannan larurar ta ciwon mama, shine suka shiga neman magani a asibiti bayan dukiyarsu ta Ƙare ƙarkaf shine suke ta yawon neman maganin Hausa ko Allah zai taimake su su yi dace.
