Cizon sauro: Nijeriya na asarar Dala biliyan 1.1 duk shekara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Lafiya na Nijeriya, Farfesa Muhammad Pate, ya ce arzikin da ƙasar take asara a shekara sakamakon cutar zazzaɓin cizon sauro ya zarta dala biliyan 1.1.

Pate ya bayyanna hakan ne yayin ƙaddamar da taron bayar da shawarwari da tuntuɓa kan yaƙi da cutar ta maleriya a Nijeriya, wanda aka yi a Abuja.

A wata sanarwa da mataimakin darektan yaɗa labarai na ma’aikatar, Alaba Balogun, ya fitar a ranar Talata, ya ce Farfesa Pate ya ce maleriya ba matsala ce ta rashin lafiya ba kaɗai ta zama matsala ga tattalin arziƙi da cigaba wadda ya kamata a ɗauki ƙwararan matakan yaƙi da ita.

Ya ce, maleriya na ci gaba da gagarumar illa a kan Nijeriya, inda take da kashi 27 cikin ɗari na yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a duniya, da kuma kashi 31 cikin ɗarin na yawan mutanen da ke mutuwa a duniya a dalilinta .

Ministan ya ƙara da cewa Nijeriya ce ta fi fama da matsalar wannan cuta, inda a 2022, sama da yara ‘yan ƙasar 180,000 ‘yan ƙasa da shekara biyar suka mutu a sanadiyyar cutar, ”wanda wannan abu ne da za mu iya kauce wa,” inji ministan.