Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu manyan malamai uku na jami’ar jihar Taraba (TSU) sun rasa rayukansu cikin sa’o’i 78.
Malaman su ne Farfesa Akporido Samuel, tsohon shugaban sashen kimiyyar sinadarai, wanda ya yi yanke jiki ya faɗi ya mutu a ofishinsa a ranar Alhamis; Dokta Kiliobas Sha’a, tsohon Shugaban Sashen Kimiyyar Halittu, da Dokta Ibrahim Saleh Bali wanda ya rasu da sanyin safiyar Lahadi.
An samu labarin cewa, Farfesa Samuel ya kwanta dama a ofishin sa yayin da Dakta Sha’a ya rasu a gidansa bayan fama da cutar hawan jini da kuma Dakta Ibrahim Saleh Bali ya rasu a FMC Jalingo bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Mutuwar malaman jami’ar ta haifar da firgici a tsakanin ‘yan uwa da ma’aikatan Jami’ar.
Malaman dai sun yi ta neman gwamnatin jihar ta inganta walwala da kuma karin albashi amma har yanzu gwamnati ta gaza biyan bukatun ma’aikatan Jami’ar.
Shugaban ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Taraba, Dakta Mbaɓe Joshua, a lokacin da yake mayar da martani game da rasuwar, ya bayyana kaɗuwarsa yayin da ya koka kan yanayin aiki da ‘ya’yan aungiyar ASUU ke ciki a cibiyar.
Ya bayyana cewa, malaman ba su da tallafin kuɗi saboda ƙalubalen tsadar rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.