Daga Sanusi Muhammad, Gusau
A ci gaba da kokarin inganta hadin gwiwar rundunar sojoji da farar hula, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar TA Lagbaja, ya raba wa yara marasa galihu 400 tufafi da takalma a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Kwamanda rundunar ta daya, 1 brigade Gusau, Brig. Janar S. Ahmed wanda ya wakilci babban hafsan soji a lokacin rabon kayan da aka gudanar a asibitin kwararru na Yariman Bakura dake Gusau ya ce, taron wani bangare ne na bikin ranar sojoji ta shekar 2024, yayinda sojojin Najeriya ke gudanar da ayyukan gaggawa ga al’ummomin da ke zaune a jihar.
Shugaban hafsan sojojin ya bayyana cewa karimcin an gudanar dashi ga al’umma ne a jihohin Kebbi da Zamfara wadanda ayyukan Yan bindiga ya shafa.
A cewarsa, an raba kayayyakin kiwon lafiya da kayan rubutu ga wasu zababbun makarantun firamare da sakandare da asibitoci a jihar Zamfara a lokacin bikin ranar sojojin.
Ya kuma koka da yadda masu baiwa ‘yan ta’adda bayanan sirri yadda rundunar sojoji suke gudanar da ayyukan su a matsayin abubuwan da ke kawo cikas ga ayyukan sojoji a Zamfara da daukacin jihohin da ‘yan taadda suka shafa a yankin Arewa maso Yamma.
Laftanar Janar Lagbaja ya bukaci al’umma a jihar Zamfara da su rika tallafa wa sojoji a kodayaushe ta hanyar ba da bayanai game da mafakar ‘yan bindiga da masu basu bayanan sirri domin mayar da martani cikin gaggawa.
