Layin mai ya dawo Abuja, yayin da ake sayar da litar mai N850

Spread the love

Dogon layi a gidajen mai ya fara dawowa a babban birnin tarayya Abuja, Niger da wasu sassa na Jihar Niger. Hakan na faruwa ne bayan gidajen mai da dama sun rufe gidajen man su. Wannan dawowar layin mai, ya sanya tsoro cikin mutane , masu abun hawa da fasinjoji.

Wannan yayi sanadiyar ana sayar da mai nera 850 a kan duk lita ɗaya a wasu gidajen man. Masu bunburutu anga sun dawo bisa hanya, wannan alama ce da ke nuna man ya fara wahala.

A bunburutu aƙalla lita na kai wa har nera 1000. Mutane da dama na kokawa kan yadda wannan tsadar man ya shafe su, kuma ya taɓa al’amuransu na yau da kullum.

Sai dai hukumar NNPCL tace har yanzu ba ta ƙara kuɗin mai ba. Kuma sun ƙara tabbatar da cewa suna da isashen mai da zai ishe su na tsawon lokaci.

By ukarofi