Cutar Ƙyandar Biri ta kama mutum 21 a Nijeriya — NCDC

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC), ta ce, mutum 21 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Ƙyandar Biri a faɗin qasar ta kuma yi ajalin mutum ɗaya daga farkon 2022 zuwa yau.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, NCDC ta ce, “zuwa yanzu, daga cikin mutum 21 da suka kamu da cutar babu wata alamar cewa sun yaɗa ƙwayoyin cutar, kuma babu wani sauyi da ya afku dangane da bayanan cutar da kuma yadda ake kula da ita.

Hukumar ta ƙara da cewa, Ƙyandar Biri cuta ce da ake samun ta a ƙasashen Afirka irin su Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da kuma Nijeriya.

Duk da dai a yankin Afirka ta ke yawo, cutar ta daga hankalin duniya bayan da aka gano sama da mutum 200 ɗauke da ƙwayar cutar a tsakanin ƙasashen duniya 19, akasari a Turai da Gabas ta Tsakiya a farkon watan Mayu. Sai babu asarar rai ko guda da aka samu.

A cewar NCDC, daga cikin mutum 61 da ake zargin suna ɗauke da ƙwayar cutar tun daga 21 ga Janairu, an tabbatar da mutum 21 sun kamu da cutar kana mutum ɗaya ya rasa ransa.

Lamarin ya shafi wasu jihohin ƙasar nan tara ne haɗe da babban birnin tarayya, Abuja.

By Editor