Cutar korona: Mutum 1 kacal ya harbu da korona cikin sa’o’i 48 a Madina

Daga WAKILINMU

Rahotanni daga Ƙasar Saudiyya, sun nuna a tsakanin sa’o’i 48 da suka gabata, mutum ɗaya kacal aka samu ya harbu da cutar korona a birnin Madina.

Bayanai sun nuna wannan wata alama ce da ke nuni da yiwuwar samun zarafin aiwatar da Hajjin bana.

A halin yanzu dai maniyyata daga sassan duniya, na ci gaba da fatan samun nasarar karya lagon annobar korona domin bada damar yin Hajjin 2021 cikin salama.