Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Cutar amai da gudawa wato Kwalara ta ɓulla a ƙananan hukumomi shida a jihar Neja, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 13, yayin da sama da 236 suna jinya a asibiti.
An fara samun rahoton ɓullar cutar ne a ƙaramar hukumar Shiroro, amma yanzu ta bazu zuwa Bosso da Minna da Magama Bida da kuma Munya.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa kwamishinan kiwon lafiya a matakin farko, Dr. Ibrahim Dangana ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa gwamnati ta ɗauki matakai daban-daban don daƙile yaɗuwar cutar.
“Mun kafa wuraren keɓance marasa lafiya a kowanne daga cikin yankunan da abin ya shafa,” inji kwamishinan.
Ya kuma ce ana gudanar da wayar da kai ga jama’a kan cutar da yadda za a kiyaye ta hannun ƙungiyoyin addini da masarautu takwas na jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma buɗe wuraren keɓance marasa lafiya a tsohuwar asibitin Idris Ibrahim Kuta da ke Minna.
Daraktan lafiyar jama’a, Dr. Ibrahim Idris, ya tabbatar da cewa Minna da Bosso da Shiroro sune wuraren da cutar ta fi ƙamari.
