Cutar sanƙarau ta ɓulla a Jigawa – NCDC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa, Dokta Ifedayo Adetifa, ya ce hukumar ta yi tattaron gaggawa sakamakon ɓullar cutar sanƙarau a Jihar Jigawa.

Dr Adetifa ya ce taron ya tattauna ƙalubale da kuma mafita dangane da ɓullar cutar a Jigawa.

Shugaban NCDC ya bayyana haka ne a shafinsa na Tiwita a ranar Lahadi.

A cewar masana, sanƙarau cuta ce wadda kan haifar da ƙagewar wuya idan ta kama mutum, wasu lokutan ma takan shafi ƙwaƙwalwa.

Masanan sun ƙara da cewa, alamomin da ke nuni da kamuwa da wannan cuta sun haɗa da; zazzaɓi, ciwon kai, amai, ƙaƙewar wuya da sauransu.