Buhari ya kafa majalisar bankwana da mulki

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya kafa majalisar da za ta lura da yadda zai miƙa mulki ga sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula a watan Mayu na 2023 bayan kammala zaɓen da za a gudanar a watan nan na Fabrairu, 2023, cikin nasara.

Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ne ya bayar da sanarwar a jiya, Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2023, mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai, Mista Willie Bassey.

Sanarwar ta ce, shi kansa Sakataren Gwamnatin ne zai jagoranci majalisar tare da Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Tarayya da Solisita Janar kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a.

Haka zalika akwai, Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Siyasa, Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaron Ƙasa (NSA), Babban Hafsan Tsaro, Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya (IGP) da Darakata Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA) duka a cikin babbar majalisar.

Daga nan sai sanarwar ta bayar da rana da lokacin da za a ƙaddamar da majalisar.

“A ranar Talata, 14 ga Fabrairu, 2023, da misalin ƙarfe 12 na rana a Ɗakin Taro na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya za a ƙaddamar da Majalisar Miƙa Mulkin. A na sa ran mambobin za su halarci rantsarwar da kansu,” inji sanarwar.

Bugu da ƙari, Shugaba Buhari ya rattaɓa hannu kan Dokar Zartarwa mai lamba 14 ta 2023, wacce ta halasta aikin Majalisar Miƙa Mulkin da kuma amincewa da tsare-tsaren miqa mulki ga sabuwar zaɓaɓɓiyar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.

Idan dai za a iya tunawa, Shugaban Ƙasa Buhari, wanda aka fara rantsar da shi a zangon farko ranar 29 ga Mayu, 2015, ya shafe kusan shekaru takwas yana mulkar ’yan Nijeriya bayan da ya sake lashe zaɓe a 2019, wanda hakan ya sake ba shi damar ƙarin shekaru huɗu bayan shekaru huɗun farko.

Kammala zango biyu a mulki shine ya ke kawo ƙarshen wa’adin mulkin Shugaban Ƙasa a Nijeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar ya tanadar. Don haka Shugaba Buhari ba shi da ikon sake tsaya wa takara a 2023 ko zarcewa bayan ranar 29 ga Mayu, 2023.

Tun daga dawowa da Nijeriya ta yi mulkin farar hula a shekarar 1999, sau ɗaya kawai Shugaban Ƙasa ya iya kammala wa’adin mulki zango na biyu.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, wanda aka zaɓa a 1999, ne ya fara kammala wa’adi na biyu a 2007. Amma magajinsa, Malam Umaru Musa Yar’Adua, ya rasu a kan mulki tun a zangon farko, inda mataimakinsa na lokacin, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya amshi ragamar mulki ya ƙarasa wa’adin farko kuma ya tsaya takara a 2011 ya lashe zaɓen.

Sai dai kuma tsohon Shugaba Jonathan bai samu nasarar zarcewa lokacin da ya tsaya takara a karo na biyu a 2015 ba, inda Shugaba Buhari mai ci yanzu ya kayar da shi a Babban Zaɓen Ƙasar da aka gudanar a shekarar. Idan Shugaba Buhari ya miƙa mulki da kansa a ranar 29 ga Mayu na 2023, zai kasance Shugaban Nijeriya na biyu a tarihi da ya tava miƙa mulki da kansa bayan kammala zango na biyu.

Kafin zuwan Obasanjo a 1999 tarihi ya nuna cewa, ba a kammala mulki zango na biyu a Nijeriya, domin Gwamnatin Jamhuriya ta Farko a ƙarƙashin jagorancin Firaminista Sir Abubaar Tafawa Ɓalewa ta fuskanci juyin mulki a zangonta na biyu ne.

Shi ma tsohon Shugaban Ƙasa, Alhaji Shehu Aliyu Shagari, sojoji sun hamɓarar da gwamnatinsa watanni kaɗan bayan ya laseh zaɓe ne a karo na biyu.