Gangamin APC ya gamu da cikas a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu

Ɗaruruwan ‘yan dabar siyasa sun haifar da cikas a gangamin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC na shiyya ta uku (Zome C).

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a garin Gashuwa, shalkwatar Ƙaramar Hukumar Bade da ke jihar Yobe, mahaifar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya.

An tsara aiwatar da gangamin ne bayan buɗe sabuwar kasuwar zamani wadda Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, ya gina a garin Nguru inda daga bisani aka hallara a Filin Agric da ke unguwar Katuzu a Gashuwa.

Bugu da ƙari, tun a garin Nguru aka fara ganin alamun yi wa tawagar ‘yan siyasar a-ture, bayan isa inda aka shirya gudanar da taron, wasu gungun fusatattun matasa suka tsaya kan hanya suna yi wa tawagar ‘yan siyasar a-ture da ihu.

Lamarin ya yi ƙamari ne a lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, yake ƙoƙarin miƙa abin magana ga Gwamna Mai Mala Buni, wanda yake tare da Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, inda kafin ka ce kwabo, fusatattun matasan suka rinƙa shewa da ihun, “ba ma yi, ba ma yi, ba ma so” tare da jifar kan mai uwa da wabi kan dandamalin da manyan baƙi suke tsaye a kai.

Kazalika, an sha ɗage ranar da za a gudanar wannan taro a jihar, sakamakon rashin tabbas da ruɗanin da APC ta shiga a jihar. Al’amarin da ya samo asali daga rikita-rikitar da ta dabaibaye zaɓen fidda-gwanin da APC ta gudanar a jihar da kuma hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa; duk suna daga cikin abubuwan da suka tunzura wasu matasa.

Har wala yau, gangamin ya samu halartar dubun-dubatar magoya bayan jam’iyyar APC a faɗin jihar, wanda ya ƙunshi jiga-jigan mutane, waɗanda suka haɗa da Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, Gwamna Mai Mala Buni tare da Mataimakinsa, Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya da shugabanin Jam’iyyar APC a jihar Yobe haɗi da kwamitin yaƙin neman zaɓen 2023 da sauransu.

Ganin yadda filin ya yamutse da ihun a-ture ya tilasta wa jami’an tsaro gaggauta arcewa da Gwamna, aka fita da shi daga wajen taron, al’amarin da ya jawo dole aka haƙura da ci gaba da taron, kowa ya kama gabansa.