
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan hidimar ƙasa (NYSC) guda ashirin da aka yi awon-gaba da su a lokacin da suke kan hanyar tafiya daga Jihar Oyo zuwa sansanoninsu a Jihar Abia sun kuɓuta bayan shafe kwana bakwai a hannun ‘yan bindiga.
An yi garkuwa da yayayyun ɗaliban ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata akan hanyar Owerri zuwa Onitsha da ke yankin Umunoha a Jihar Imo, bayan wasu ‘yan bindiga sun farmaki motocin bos biyu da ke ɗauke da su daga Ibadan, inda suka tasa ƙeyarsu su 20 zuwa daji. Wannan al’amari ya haifar da damuwa acikin iyalansu da kuma fargabar halin amincin matasan ‘yan Nijeriya da ke tafiye-tafiye zuwa wuraren ayyukan hidimar ƙasa.
Da fari, jimillar abin da ‘yan bindigar suka buƙaci a biya shi ne Naira biliyan ɗaya ga ‘yan hidima 20, wato miliyan N50 ga kowanne, inda daga bisani kuma aka dawo da shi miliyan N100.
Saidai, ba a bayyana ainihin yadda al’amarin shaƙar ‘yancin ‘yan hidimar ya kasance ba yayin haɗa wannan rahoto. Tuni dai aka garzaya da su Babban Asibitin Owerri da ke Imo, inda ake duba lafiyarsu.
Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ya ziyarci ‘yan hidimar a asibitin, inda ya samu rakiyar kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, daraktan DSS da kwamandan sojoji na Artillery Brigade ta 34.
