
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ƙwararren harkar ci-gaban al’umma kuma ɗan siyasa a Jihar Ribas, Blessing Fubara, ya bar jam’iyyar APC a hukumance inda ya koma NDC a wani yanayi na haɗa hannu ‘yaj ɓangaren adawa yayin tunkara zaɓen 2027.
Fubara, wanda ɗan uwa ne ga gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya sanar da wannan mataki ne a Abuja, inda aka karɓi baƙuncinsa a jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa Seriake Dickson da wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Ya ce, ya yanke hukuncin ne saboda damuwa da makomar siyasa da ɗorewa al’amura a Jihar Ribas yayin da ake cigaba da samun fargaba.
Fubara, ya kuma bayyana cewa jihar za ta samu gagarumar sauyi na ci-gaba bayan zaɓen 2027.
Jigon siyasar ya yi digirinsa ne akan Ci-gaban Al’umma da Ilimin Manya. Sannan, shi ne Darakta Manaja kuma Shugaban Kamfanin D’Congsiglories LLC.
