Da Ɗumi-Ɗumi: Duk da umarnin kotu, Ibas ya naɗa jagororin ƙananan hukumomin Ribas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jagoran da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a Jihar Ribas, VA Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya naɗa jagorori a ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Haka kuma ya saki marar jagororin hukumomi da ma’aikatun jihar da aka dakatar da su a baya, kamar ya bayyana a wata sanarwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin jagororin zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Afrilu, wato kwanaki biyu da suka gabata.

Hakan ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya dake Fatakwal ne na hana jagoran naɗa jagororin ƙananan hukumomin.

Mai Shari’a Adamu Turaki Muhammad ya bada umarnin hakan bayan shigar da ƙara da Shirin ‘Civic Education Initiative’ daga Cibiyar PILEX ya yi a ƙarƙashin jagorancin Courage Msirinmovu.

Ya ƙalubalanci hukuncin Ibas ne da aka naɗa na wata shida na ƙoƙarin naɗa jagorori a ƙananan hukumomin.

Bayan hukuncin hana jagoran ne, kotun ta kuma zaɓi ranar 14 ga Afrilu, 2025 don sake zama akan batun.

By Babaji