Da Ɗumi-ɗumi: Gobara ta tashi a Kasuwar Abgeni a Oyo

Kasuwar Agbeni da ke Ibadan, Jihar Oyo, ta kama da wuta.

Manhaja ta tattaro cewar gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 04:30 na asuba a ranar Lahadi.

Shugaban Hukumar Kwana-kwana na yankin, Yemi Akinyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce, “Har yanzu jami’anmu na ci gaba da aikin kashe gobarar.”

Ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga tantance ɓarnar da gobara ta tafka a kasuwar ba.