Batun ƙarin albashin likitoci

Buƙatar da likitoci suka yi na neman a ninka masu albashinsu ninki biyu, ya sake dawo batun yanayin aikin likitoci a Nijeriya. Likitocin sun ɗora buƙatarsu kan taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar. Wannan ya haɗa da ƙarancin darajar Naira da illar da ta ke yi wajen tsadar rayuwa a ƙasar.

Sun koka da cewa, duk da cewa an yi yarjejeniya da gwamnati don sake duba tsarin albashin da ake biyansu (CONMESS), wanda aka yi nazari a baya sama da shekaru 10 da suka wuce, gwamnati ta kasa magance matsalar. Don haka sun ba gwamnati wa’adin makonni biyu don magance buqatunsu ko kuma su ɗauki mataki.

Baya ga buƙatar ƙarin albashi, sun tunatar da a basu kuɗin Horar da Ma’akatan Kiwon Lafiya (MRTF) na shekarar 2023, wanda aka yi yarjejeniyar da ministan lafiya. Sun buƙaci a biyasu cikon kuɗin albashinsu na 2014, 2015 da 2016, da kuma daidai ta ƙarin kuɗin albashi da aka yi. Kuma sun ja kunne kan yadda gwamnoni ke iya barci bayan rashin kula da lafiyan mutane.

Akan lasisin aikin likita bayan yin aiki na shekara biyar da Majalisan tarayya ta kawo. Sun ce ba za su lamunta ba. Dan dokar za ta mai da likitocin bayi ne.

Kuma sun nemi a ɗauki aiki a asibitocin da ke da ƙarancin ma’aikata, Kuma a yi gyaran asibitocin don inganta aikin jami’an lafiya da kuma samun lafiyar mutane.

Gwamnati na ganin ba zai yiwu a biya buƙatar likitocin gaba ɗaya ba, inda aka bada rahoton cewa an qara masu kashi 25 cikin ɗari. Likitocin dai ba su amince da hakan ba, inda suka ce Gwamnatin Tarayya za ta iya biyan dukka buƙatarsu. Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NARD), Emeka Orji, ya shaidawa gidan talabijin na aasa kwanan nan cewa al’amura suna ƙara ta’azzara kuma babu wani ƙarin albashin da gwamnati ta yi masu.

Muna tsammanin za a iya daidaitawa game da buƙatar ƙarin kashi 200 na albashin likitoci. Ya kamata gwamnati da likitoci su zauna don tattaunawa da gaskiya, su cimma matsaya ta gaskiya. Yajin aiki na yau da kullum ba shi ne mafita ga kowace matsala ba.

Matsalar ita ce Gwamnatin Tarayya ba ta nuna daraja yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyoyi da dama. Misali ta soke yarjejeniyar da ta ƙulla da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), wanda hakan ya sa ƙungiyar ta tsunduma yajin aikin da ya jawo gurgunta ayyuka ilimi a jami’o’in ƙasar. Likitoci su ma sun samu dalilin shiga yajin aikin saboda gazawar gwamnati wajen cika yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar.

A cikin watan Yunin 2020, lokacin da COVID-19 da ta addabi duniya, ƙungiyar likitoci ta shiga yajin aikin gama-gari bayan cikar wa’adin kwanaki 14 ga Gwamnatin Tarayya. Yajin aikin ya shafi dukkan asibitocin tarayya da na jihohi.

Wani ɓangare na ƙorafin likitocin shi ne cewa babu wani tsari na tallafawa iyalansu bayan sun mutu.

Har ila yau, sun koka da yadda ake ba su alawus-alawus, rashin biyan basussukan albashin da su ke bi manyan wuraren kiwon lafiya na tarayya da na jihohi da kuma rashin aiwatar da dokar horar da ma’aikatan lafiya a asibitocin tarayya da na jihohi. Tun daga wannan lokacin, likitocin sun sami dalilin shiga yajin aikin saboda wani dalili ko wani.

A cikin Afrilu 2021, gwamnati da likitocin da suka shiga yajin aiki sun amince da yarjejeniyar fajimtar juna, inda likitocin suka dakatar da yajin aiki na mako guda. Amma daga baya gwamnati ta yi watsi da yarjejeniyar da ta yi da likitocin.

A yau, irin waɗannan batutuwan ba a gama warware su ba. A bayyane yake cewa gwamnati ta yi watsi da fannin kiwon lafiya tsawon shekaru. Kasafi a fannin ya kai kusan kashi biyar cikin zari duk da yarjejeniyar da ƙasashen Afirka suka yi a Abuja a shekara ta 2001 cewa kashi 15 cikin 100 na kasafin kowace ƙasa ta tafi wurin kiwon lafiya. A bana, kasafin Kuɗin da aka ware wa kiwon lafiya ya kai kashi 5.7 bisa xari.

Bayan haka, albashin likitoci ba ishensu. Hakan ya haifar da ficewarsu zuwa wasu ƙasashen duniya. Dubban likitocin Nijeriya ne ke yin qaura zuwa ƙasashen Amurka, Ingila, Australia, Kanada, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Kuwait, Saudiyya da sauran ƙasashe da dama.

Masana sun kiyasta cewa tara a cikin 10 likitoci suna la’akari da damar aiki a ƙasashen waje. Hakan na faruwa ne duk da biliyoyin daloli da aka kashe don horar da waɗannan likitoci. Sakamakon ya nuna cewa adadin majinyata da likitoci ya kai kusan 1:5,000 a Nijeriya saɓanin 1:600 da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da shawarar.

Akwai buqatar tattaunawa tsakanin likitoci da gwamnati. Ya kamata gwamnati ta ci gaba da daraja yarjejeniyarta da likitoci. Jama’a su amince da gwamnati a duk lokacin da ta yi alƙawari.

Ya kamata a magance wa’adin yajin aikin da zai ƙare a ranar 13 ga Mayu. Domin kuwa duk wani yajin aiki a yanzu zai wahalar da talakan da ba zai iya biyan kuɗin asibitoci masu zaman kansu ba. Ga waɗanda aka kwantar da su a asibitocin gwamnati, za a iya sallamar su idan aka yi yajin aiki. Ba za mu iya ci gaba da wasa da tsarin lafiyarmu ba. Wannan shi ne lokacin gyara.