Matashin nan ɗan Jihar Kano wanda ya auri baturiya a lokutan baya, wato Suleiman Isah, ya zama sojan Amurka.
A ranar 13 ga Disamban 2020, aka ɗaura auren Isah da Janine Reimann, a lokacin yana ɗan shekara 23 yayin da matarsa ke da shekara 46.
Ma’auranta sun haɗu ne a soshiyal midiya a dandalin Instagram inda suka taɓa soyayyar wata 10 kafin su yi aure.