’Yan bindiga sun sako mutum 28 cikin 40 da suka sace a cocin Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu mutane 28 da aka yi garkuwa da su a wani coci a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu, 2023, sun shaƙi iskar ’yanci.

Waɗanda sakon ɗin sun haɗa da ƙananan yara, waɗanda aka yi garkuwa da su a wani coci a ranar Lahadin da ta gabata, aka kai su inda ba a san ko ina ne ba.

Sai dai wani babban jami’in ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an sako 11 daga cikin waɗanda aka kashe a daren Laraba.

Ko da yake hukumar ’yan sandan ba ta ce uffan kan lamarin ba, majiyar ba ta bayyana ko an biya kuɗin fansa ga ’yan bindigar ba kafin a sako waɗanda abin ya shafa ko akasin haka.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, 28 daga cikin 40 da aka yi garkuwa da su sun samu ’yancinsu yayin da wasu 14 ke hannun su.