’Yan bindiga sun sace sama da mutum 40 a Neja

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun sace Dagacin ƙauyen Fugge, Malam Abdullahi Zaure, cikin Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja.

Bayanai sun ce maharan sun kuma haɗa da wasu mutum 49 sun yi awon gaba da su.

Rahotanni daga yankin sun ce waɗanda ‘yan bindigar suka kwashe a harin na ranar Juma’a, sun haɗa da mata da ƙananan yara da kuma maza ƙalilan.

Kazalika, an ce maharan sun tattara shanu a yankin sun yi gaba da su.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar, maharan sun kai hari ƙauyen ne da tsakar rana a kan babura inda suka yi harbe-harben bindiga a iska don razanarwar.

Majiya mai tushe ta ce an ga jirgin yaƙin sojoji ya bibiyi sawun ɓarayin a yankin.

“Yayin harin, jirgin yaƙin sojojin ya yi luguden wuta a kan ‘yan bindigar a lokacin da suke ƙoƙarin wucewa da mutane da kuma shanun da suka sata. Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin maharan da ma shanun da suka kora.

“Mun ga wasu gawarwakin ‘yan bindigar da na shanun da suka mutu a dajin da jirgin ya yi luguden wuta.

“Bayan harin da jirgin ya kai, ‘yan bindigar sun tsere sun ɓoye a maɓuyarsu a dajin da ke tsakanin Jihar Neja da Kebbi,” in ji majiyar.

Ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin ’Yan Sandan jihar, DSP Abiodun Wasiu, ya ci tura.