
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar da tsare-tsaren babban zaɓen 2027, ciki har da lokutan kaɗa ƙuri’a, zaɓen fidda gwani, yaƙin neman zaɓe da kuma rajistar masu zaɓe.
Hakan na zuwa ne yayin da al’umma ke cece-kucen jinkirin kammala aiki akan ƙudirin gyaran dokar zaɓe a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Tun a ranar 4 ga watan Fabrairu ne INEC ta ce, ta kammala aiki akan jaddawalin tsare-tsaren zaɓukan duk da jinkirin gyaran dokar zaɓen.
A cewar jaddawalin na INEC, za a gudanar da zaɓen Shugaba ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin ƙasa a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027. A ranar 6 ga Maris kuwa, wato makonni biyu bayan na farkon, za a yi na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.
Haka kuma, hukumar ta bayyana lokacin gudanar da yaƙin neman zaɓe a hukumance ga jam’iyyu da ‘yan takara. Na shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin ƙasa zai fara ne daga 18 ga Nuwamban 2026, wanda za a ƙarkare a 19 ga Fabrairun 2027.
Sai kuma na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, wanda za a fara daga 15 ga Disambar 2026, a kuma kammala a 5 ga Maris, 2027, wato sa’o’i 25 kafin gudanar da zaɓe.
A wani ɓangare na shirye-shiryen zaɓen, INEC ta sanar da cigaba da yi wa masu zaɓe rajista (CVR), inda za a ɗora daga inda aka tsaya a watan Afrilun 2026, sannan a kammala a Junairun 2027, matakin da ya ba ‘yan Nijeriya da suka cancanta damar rajista da gyara bayanan katin zaɓensu.
Kazalika, an ba jam’iyyun siyasa damar yin zaɓukan fidda gwani daga ranar 1 ga Yuli zuwa 30 ga Satumba a 2026. Baya ga haka, wajibi ne su miƙa jaddawalin ‘yan takararsu ga hukumar a tsakanin 1 da 31 ga watan Oktoba, 2026.
