
Daga RABI’U SUNUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada ƙudirinta na ƙarfafa tsaro acikin al’umma ta hanyar cigaba da tallafa wa ƙungiyoyin tsaro na sa-kai a faɗin jihar.
A wani mataki na ƙara ƙarfafa ayyukan tsaro, Mai Bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf Shawara kan Tsaron Al’umma (Community Policing), Dr. Maimunat Umar Sharif, ta miƙa tallafin kuɗi har na ₦500,000 ga Hedikwatar ’Yan Banga ta Jihar Kano.
Tallafin na da nufin inganta ƙarfin aikin ’yan banga domin su ci gaba da taka rawar gani wajen magance matsalolin rashin tsaro a matakin al’umma.
Dr. Sharif ta bayyana cewa wannan tallafi na nuna yadda gwamnatin jihar ke daraja muhimmiyar rawar da ’yan banga ke takawa wajen tallafa wa hukumomin tsaro, musamman ta fuskar tattara bayanan sirri da kuma ba da amsa cikin gaggawa.
Ta ƙara da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa ƙungiyoyin tsaro na al’umma a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Kano.
A nasa jawabin, Kwamandan Kungiyar ’Yan Banga ta Jihar Kano, Ambasada Shehu Muhammad Rabiu, ya yabawa gwamnatin jihar bisa ci gaba da ba su goyon baya.
Ya bayyana cewa baya ga tallafin kuɗi, gwamnatin ta kuma samar masu da ofis da wasu muhimman kayan aiki da suka taimaka matuƙa wajen inganta ayyukansu.
Ambasada Rabiu ya tabbatar da cewa ’yan banga za su ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
