
Daga BELLO A. BABAJI
Da misalin ƙarfe 2:05 na ranar Litinin ne jami’an Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA) suka rufe Hedikwatar babbar jam’iyyar adawa, PDP dake yankin Wuse a Abuja.
A ranar Juma’a ne rahotanni suka bayyana cewa, FCTA a ƙarƙashin umarnin Ministan Abuja, Nyesom Wike za ta fara ƙwace filaye daga ranar Litinin, wato yau, a sakamakon rashin biyan kuɗaɗen hayar ƙasa na shekaru tsakanin 10 da 43.
Filin Hedikwatar PDP yana ɗaya daga cikin wuraren da aka zayyano, wanda a watan Maris, 2025 ne aka ƙwace shi saboda rashin biyan kuɗin hayar ƙasa.
A yayin ganawa da manema labarai ne a ranar Juma’a mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka; da Daraktan kula da filaye, Chijioke Nwankwoeze; da kuma Daraktan kula da lamuran Ci-gaba, Mukhtar Galadima suka bayyana hakan.
Sun ce, an yanke hukuncin karɓe filayen ne a ƙarƙashin dokokin gudanarwa, lamarin da ya sa babu ɗaga ƙafa ga kowaye hakan ya shafa.
