
Daga BELLO A. BABAJI
Wata Babbar Kotun Shari’a a Kano ta yanke wa Shafi’u Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa cinna wa masallata wuta a wani masallaci dake Ƙauyen Gadan a Ƙaramar Hukumar Gezawa ta jihar.
Lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mutane ke tsaka da yin sallar Asuba a ranar 15 ga watan Mayu, 2024.
Kimanin mutane 11 ne suka rasa rayukansu a yayin karɓar magani a Asibitin Murtala Muhammed.
Alƙali Halhatu Huza’i Zakariya, a lokacin da aka gurfanar da Abubakar, ya yanke masa hukuncin ne, bayan samun sa da laifuka huɗu da ake tuhumar sa a kansu.
Laifukan sun haɗa da kisa mara dalili, yunƙurin kisa, sabbaba raunatawa da kuma ɓarna da wuta waɗanda sun saɓa wa sashe na 143, 148 da na 370 na kundin shari’a ta jihar ta 2000.
Kotun ta kuma umarci a yi wa mai laifin bulala 100 da ƙarin 50 da kuma cin sa tarar Naira 1,500.
Haka kuma ta umarci a ƙwace babur ɗinsa a bai wa gwamnatin jihar, wanda da kuɗinsa ne za a gyara damejin da aka yi wa masallacin.
A ranar 25 ga watan Mayu, 2024 ne aka gurfanar da Abubakar, inda ya amsa aikata laifuka uku da aka fara tuhumar sa a kai da suka yi sanadin mutuwar mutane sha ɗayan.
