Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta aika masu zanga-zangar matsin rayuwa gidan kaso na Kuje

Spread the love

Wasu daga cikin masu zanga-zangar mastin rayuwa da aka gudanar a watan da ya wuce an tura su gidan kaso na Kuje.

Mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun da ke Abuja ya yanke wannan hukuncin bayan da aka tuhume da cin amanar ƙasa. Mai shari’an ya bayyana zai fara sauraren belin su ranar 11 ga watan Satumba 2024.

Wannan ya biyo bayan zargin su da ake da cin amanar ƙasa da ƙoƙarin tada zaune tsaye.

Mutum goma da su ka bayyana gaban kotu sun haɗa da Micheal Adaramoye wanda a ka fi sani da Lenin, Adeyemi Abayomi, Suleiman Yakubu, Opaoluwa Simon da Angel Innocent.

Saura sune, Buhari Lawal,Moisu Sadiq, Bashir Bello, Nuradeen khamis da Abdulsalam Zubairu.

Ana zarginsu da laifuka shida da suka haɗa da cin amanar ƙasa, yunƙurin tada zaune tsaye, ji wa ƴan sanda ciwo da sauransu. Duk waɗannan laifuka ne da ke da hukunci a ƙarƙashin sashi na 97 a dokar Penal Code.

By ukarofi