
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rundunar ƴan sanda ta shelanta neman wani ɗan Burtaniya mai suna Andrew Wynne kan zarginsa da kitsa kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
An gano cewa rundunar ta gudanar da wani bincike kan yadda wasu ƴan ƙasashen waje suka kitsa kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Nijeriya.
Mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya faɗi haka a hedikwatar rundunar da ke Abuja inda ya ce ɗan Burtaniyan ya karɓi hayar waje ne a ‘Labor House’ da ke Abuja inda a nan ya ke ayyukansa na zamba cikin aminci yayin da ya fakewa da sunan gudanar da harkokin karatu.
Ya ce, bayan wani bincike na sirri ne da aka gudanar tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro, aka yi nasarar kama mutum tara da hannu a cikin shirin waɗanda ke karɓar tallafi na kuɗi daga wasu mutane daga wajen Nijeriya kan rikita al’amuran ƙasar.
Binciken ya kuma nuna cewa suna da hannu a tallafa wa tashin-tashina acikin zanga-zanga, yaɗa labaran ƙarya da sauran laifukan da ke tabbatar da shirinsu na kifar da gwamnatin.
