Motocin yaƙi da ‘yan ta’adda suka ƙona an bar su ne lokacin da suka lalace – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Hedikwatar tsaro ta fito ta bayyana cewa motocin yaƙi da ‘yan ta’adda su ka ƙona a wani faifan bidiyo dama sun lalace ne.

Wannan ya fito a wani bayani da daraktan yaɗa labarai na tsaro Manjo Janar Edward Buba a ranar Litinin.

Buba ya ce, ma’aikatan “Operation Hadarin Kaji” a ranar 29 ga Agusta a yayin da suke wani sintiri a ƙauyen Kwashabawa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara. Ya bayyana motocin sun lalace ne a wannan hanyar saboda faɗawa da su kai cikin taɓo.

Buba ya cigaba da faɗa cewa sannan wani faifan bidiyo da ke yawo yana nuna an kashe mutane a Sokoto yace ƙarya ne.

By ukarofi