Gwamnatin Katsina ta kashe biliyan N30 a harkar tsaro cikin shekara ɗaya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Dikko Raɗɗa ta kashe Naira biliyan 30 a cikin shekara ɗaya da watanni uku kan harkar tsaro.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Dr Nasir Mu’azu Ɗanmusa ne ya faɗi haka a taron masu ruwa da tsaki na shiyyar Funtuwa da Gwamna Raɗɗa ya jagoranta.

Kwamishinan ya bayyana cewa, a duk wata gwamnatin jihar na bai wa ƙananan hukumomin da rashin tsaro ya shafa Naira Miliyan uku, domin sayen man fetur na sintiri.

Ya yi cikakken bayani akan halin da suka sami jihar akan matsalar ta’addanci da ƙokarin da gwamnatin ta yi na magance matsalar.

Dr. Ɗanmusa ya yi gwamnati a shirye ta ke ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga al’ummar jihar baki ɗaya musamman ƙananan hukumomin da suke fama da matsalar tsaro.

Wannan shine karo na farko da Gwamna Dikko Raɗɗa ya fara rangadin ƙananan hukumomi 34 da suke jihar, domin yi wa al’umma bayanai kan yadda gwamnatin jihar ta Katsina ke yi da kasafin kuɗin 2024.

By ukarofi