Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tabbatar da Adeleke a matsayin Gwamnan Osun

Spread the love

Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da Adegboyega Oyetola na Jam’iyyar APC ya ɗaukaka inda yake ƙalubalantar nasarar da Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP ya samu a matsayin Gwamnan Jihar Osun.

Da yake karanto hukuncin yayin zaman kotun a ranar Talata, Mai Shari’a Emmanuel Agim ya tabbatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke na cewa Adeleke shi ne wanda ya yi nasara a zaɓen na Osun.

Kotun Ƙolin ta ce mai ƙara ya gaza gabatar wa kotun gamsassun hujjoji kan zargin da ya yi cewa an zuba ƙuri’a wuce kima a zaɓen gwamnan jihar Osun da ya gudana ran 16 ga Yulin 2022.

Don haka duka alƙalan da ke sauraren shari’ar su biyar suka tabbatar da nasarar Adeleke.

By Editor