Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Birtaniya ta ɗaure Ekweremadu shekara 10 a kurkuku

*Matarsa, Beatrice za ta shafe shekara shida a gidan yari

Kotun Birtaniya ta ɗaure tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, shekara 10 a gidan yari kan yunƙurin cire sannan mutum.

Kazalika, kotun ta yanke wa matarsa, Beatrice, ɗaurin shekara shida a kurkuku.

Kotun ta kama Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice da Dr Obinna Obeta, da laifin safarar sassan mutum ƙarƙashin Dokar Safarar Bayi na Zamani.

Kotun ta same su da laifin haɗin baki wajen ɗaukar wani matashi ɗan shekara 21 daga Legas zuwa wani asibitin London don cire masa ƙodar da za a dasa wa ‘yar Ekweremadun, Sonia.

Da yake yanke hukuncin a ranar Juma’a, Alƙalin kotun, Mr Jeremy Johnson, ya ce baki ɗaya su ukun sun taka rawa wajen aikta laifin.

Ya ce, “Cire sassan mutum nau’i ne na safarar bayi. Ana ɗaukar sassan jikin mutane tamkar kadara ana sayarwa.”