Kamfani Max Air zai yi jigilar Mahajjatan Kano – NAHCON

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Alhazai ta Nijeriya, NAHCON, ta naɗa kamfanin Max Air a matsayin kamfanin jigilar maniyyatan Jihar Kano 5,917 zuwa ƙasar Saudiyya a lokacin aikin Hajjin bana.

Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Ɗambatta ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Kano.

Ya ƙara da cewa, kamfanin yana da inganci kuma yana da jiragen sama uku masu ƙarfin iya jigilar mahajjata sama da 1000 kowanne.

Jaridar ta tuna cewa hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano da gwamnatin jihar sun yi maraba da matakin da NAHCON ta ɗauka na bai wa kamfanin Azman Air jigilar Alhazan jihar a bara.

Kamfanin Max Air dai ya daɗe yana jigilar alhazan jihar zuwa aikin Hajji har zuwa shekarar da ta gabata a lokacin da shugabancin NAHCON na wancan lokaci ya bai wa kamfanin Azman Air, matakin da jihar ta bijire.

Hakazalika, Ɗambatta ya kuma sanar da cewa hukumar ta rufe sabon rajistar aikin Hajji bisa ga umarnin NAHCON.

A cewarsa, alhazan jihar sun ci gajiyar kusan guraben aikin Hajji 6,000 da hukumar alhazai ta ware musu, inda ya ƙara da cewa maniyyata 4,900 ne suka kammala biyan kuɗin aikin Hajjin nasu, yayin da sauran waɗanda suka ajiye Naira miliyan 2.5 kowanne zai biya sauran kwanaki biyu masu zuwa.

Sakataren zartarwa ya kuma bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da aikin Hajjin bana, inda ya ce “mun kammala dukkan shirye-shirye tun daga masauki, ciyarwa, jigilar kaya daga Jeddah zuwa Makkah da Makkah zuwa Madina.

“Muna shirye don tashin jirgi, mun yi tsari mai kyau wanda zai tabbatar da kuɗin da mahajjatan mu ke biya. Mahajjatan mu za su yi rayuwa mai kyau a Saudiyya,” in ji shi.