Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Sodangi ya riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa Sanata Abubakar Danso Sdangi rasuwa.

Ya rasu ne ranar Lahadi da daddare, inda ya bar duniya yana da shekara 70.

A halin rayuwarsa, Marigayin jigo ne a jam’iyyar APC a shiyyar Nasarawa ta Yamma.

Kuma shi ne Shugaban Kwamitin Neman zaɓe na Gwamna Abdullahi Sule a 2023.

Ya wakilci shiyyar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa na tsawon shekara 12.