Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Rahotanni daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa sama da mutane miliyan 113 a faɗin ƙasashe 53 ne suka fuskanci matsananciyar yunwa a shekarar da ya gabata a sanadiyyar yaƙe-yaƙe, annoba da kuma matsalolin tattalin arziki wanda ke haddasa ƙarancin abinci.

Aqalla ’yan Nijeriya miliyan 25 ne ke fama da yunwa, yayin da mutane miliyan 9.3 ke fama da matsanancin ƙarancin abinci, wanda hakan ya sa ake ta samun zanga-zanga da fasa rumbunan adana abinci a wasu sassan ƙasar, daidai lokacin da ƙasar ke tsaka da fama da tashen-tashen hankula na masu ɗauke da makamai.

Nijeriya na fuskantar rikici daga kowane vangare, wanda ke daqile hanyoyin cigaban ƙasar. Ba wai hedikwatar talauci ta duniya ba ce kawai, har ma ta shiga cikin jerin ƙasashen da suka ɗaga tuta a matsayin wuraren da ake fama da yunwa a duniya. A wani rahoton haɗin gwiwa da Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta fitar sun bayyana cewa, matsalar ƙarancin abinci ta qara tsananta a Nijeriya da wasu ƙasashe 18.

Rahoton ya ƙara da cewa, ana sa fargabar adadin mutanen da ke fuskantar matsananciyar qarancin abinci a duniya zai cigaba da ƙaruwa a kullum. Daga cikin ƙasashen da ke fuskantar wannan matsala bayan Nijeriya akwai Afghanistan, Habasha, Somaliya, Sudan ta Kudu, da Yemen. Kuma yawancin waɗannan ƙasashe sun gaza.

Darakta Janar na FAO, QU Dongyu, ya ƙara da cewa, tsananin fari da ake fama da shi a yankin kahon Afirka ya jefa mutane cikin halin yunwa, tare da lalata amfanin gona da kashe dabbobin da rayuwarsu ta dogara da su. “Mutanen da ke cikin ƙasashe mafi talauci musamman waɗanda har yanzu ba su murmure ba daga tasirin cutar ta COVID-19 suna fama da rikice-rikicen da ke faruwa ta fuskar ƙaruwar farashin kayan abinci da taki, gami da vacin yanayi.”

Darakta Janar na FAO, QU Dongyu, ya ƙara da cewa, tsananin fari da ake fama da shi a yankin kahon Afirka ya jefa mutane cikin halin yunwa, tare da lalata amfanin gona da kashe dabbobin da rayuwarsu ta dogara da su.

“Mutanen da ke cikin ƙasashe mafi talauci musamman waɗanda har yanzu ba su murmure ba daga tasirin cutar ta COVID-19 suna fama da rikice-rikicen da ke faruwa ta fuskar ƙaruwar farashin kayan abinci da taki, gami da vacin yanayi.”

A cikin wani rahoto da ta fitar a shekarar da ta gabata, wata cibiyar bincike ta ƙasar Birtaniya mai suna Institute of Development Studies (IDS), ta sanya Nijeriya a matsayin ƙasa ta biyu mafi talauci a duniya da samun tsadar abinci. Ƙasa ta ɗaya ita ce Syria. Nijeriya ta kuma kasance cikin jerin ƙasashe 10 da suka fi fama da yunwa a cikin jerin ƙasashe masu fama da yunwa a duniya. Yankin da ya fi muni shi ne Arewa maso Gabas inda sama da mutane miliyan huɗu ke fuskantar barazanar qarancin abinci. Jihohin da suka fi muni su ne Adamawa, Borno da Yobe. Matsalar yunwa dai na qara ta’azzara ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, musamman hauhawar farashin kayan masarufi wanda ya zuwa watan Fabrairun bana.

Matsalar rashin tsaro ita ce babbar silar da ta haifar da yunwa. A matakin duniya, yaqin da ke tsakanin Rasha da Yukren shi ne babban al’amari. Yukren dai ita ce babbar mai fitar da alkama. A Nijeriya, matsalar tsaron cikin gida ya haifar da yaƙi. A duk faɗin ƙasar, ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun sanya rayuwa ta yi wahala ga ‘yan ƙasa. Kullum suna garkuwa da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, ba dare, ba rana. A kan saki waɗanda suka yi sa’a bayan an biya ’yan ta’addar kuɗin fansa mai yawa. Waɗanda aka yi rashin sa’a kuwa an kashe su. An kashe dubban mutane. Miliyoyin wasu kuma sun rasa matsugunansu inda su ke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira daban-daban, ciki har da wajen ƙasar.

A wasu sassan ƙasar kuma, ’yan ta’adda sukan kai hari kan manoma, lamarin da ya kori da yawa daga cikin manoman daga gonakinsu. A shekarar 2020 ne ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai mummunan hari a wata gona a qauyen Zabarmari da ke ƙaramar hukumar Jere a jihar Borno, inda suka kashe ma’aikatan gona aƙalla 67. Ga wasu daga cikin waɗanda suka tsere daga harin ‘yan ta’addan, baƙin cikinsu shi ne lalata amfanin gonakinsu da shanu. A wurare irin su Zamfara ana tilastawa manoma da sauran mutanen qauye biyan haraji ga ’yan ta’addan domin a barsu zuwa gonakinsu.

Babban dalilin wannan matsalar tsaro shi ne rashin aikin yi. Wani ƙiyasi ya nuna cewa, yawan marasa aikin yi a Nijeriya ya haura kashi 60 cikin ɗari. Kasancewar yawancin matasa ba su iya samun aikin yi ba, suna ƙirƙirar wa kansu aiki a masana’antun aikata laifuka.

Noma, wanda zai iya zama alheri kuma ceto ga ƙasa, an yi watsi da shi saboda yawancin matasa ba sa son sa. Sun gwammace ayyukan albashi wanda ya yi ƙaranci a kwanakin nan.

A halin yanzu dai ’yan Nijeriya da dama musamman matasa na ficewa daga ƙasar. Ƙwararrunmu, musamman likitoci, suna ƙaura zuwa ƙasashen waje don yin aiki saboda ba su samun isasshen kuɗi a gida. Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare kuma ya yi illa ga dukiyar ƙasa.

Ba zato ba tsammani, noma ya kasance babbar hanyar magance yunwa a Nijeriya. Don haka ya kamata gwamnatoci a dukkan matakai su ƙarfafa gwiwar manoma ta hanyar samar musu da isasshen tsaro. Su kuma fito da tsare-tsare don magance matsalar abinci, kamar aka fara a cikin watannin nan.

Ya kamata gwamnati ta kuma yi la’akari da bada ƙwarin gwiwa ga manoma. Muna da isasshen fili don noman abinci kuma dole ne mu yi wani abu don zamanantar da noma ta hanyar tura fasahar zamani. Ya kamata manoma su rungumi noma da injunan noma na zamani. Kamfanonin iri ya kamata su mai da hankali kan nau’ikan da aka ƙirƙira ta kwayoyin iri waɗanda za su inganta amfanin gona.

Mun yaba wa Bankin Raya Afirka (AfDB), wanda aka bayar da rahoton ya ƙaddamar da dala biliyan 1.5 na samar da abinci na gaggawa na Afirka don hana matsalar abinci da ke kunno kai. Muna kira ga sauran manyan ƙungiyoyi su kawo agaji ga ƙasashen da abin ya shafa.