Zargin Cushen Kasafi: Ningi na fuskantar haɗarin dakatarwa daga Majalisa

*Gobe Majalisa za ta yi zama kan zargin

Daga BASHIR ISAH

Ya zuwa ranar Talata,12 ga Maris, ake sa ran Majalisar Dattawa za ta yi zama kan zargin da Sanata Abdul Ningi (PDP Bauchi ta Tsakiya) ya yi inda ya ce an yi cushe a kasafin 2024.

A hirar da BBC Hausa ta yi da shi a ƙarshen mako, an jiyo Sanata Ningi ya yi zargin cewa, kasafin 2024 da Majalisa ta amince da shi tiriliyan N25 ne, amma wanda ake aiki da shi tiriliyan N28.7.

Ya ce, “A karon farko a tarihin Nijeriya, yau muna amfani da kasafi guda biyu mabambanta. Na farsko shi ne wanda Majalisa ta amince da shi kuma Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu, gudan kuma shi ne fadar shugaban ƙasa ke aiki da shi.

“Kasafin tiriliyan ₦25 shi ne wanda muka amince da shi, yayin da Gawamnatin Tarayya ke aiki da kasafin tiriliyan ₦28.

“Mun gano an yi cushe na tiriliyan ₦3 ba tare da ayyana wurare ba. Wannan shi ne cushe mafi girman da ya auku a tarihin Nijeriya.

“A matsayinmu na wakilan jama’a, mun yanke shawarar ganawa da Shugaba Tinubu kan wannan batu, don mu tambaye shi shin ko ya san da abin kunyar da aka aikata ko kuwa a’a, sannan daga nan za mu ɗauki matakin da ya dace.

“’Yan Nijeriya su yi haƙuri da mu, saboda wannan batu ne da ya shafi ƙasa da ‘yan baki ɗaya, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya, yare, ko addini ba,” in ji Ningi.

Kodayake, Majalisar Dattawar ta bakin Kakakinta, Sanata Yemi Adaramodu (APC Ekiti ta Kudu), ta musanta zargin a ranar Asabar da daddare.

Kawo yanzu dai Majalisar ta kama hanyar ɗaukar matakan da take ganin sun dace a kan Ningi kan zargin da ya yi.