Jami’an tsaro sun kashe tsegerun IPOB 20, sun dagargaza sansanoninsu

Daga BASHIR ISAH

Dakarun haɗin gwiwa ƙarƙashin Operation Udoka da ya ƙunshi ‘yan sanda, DSS da jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence, sun kashe tsegerun IPOB/ESN mutum 20 a wani samamen da suka kai maɓuyar ‘yan ta’addan da ke yankin Ƙaramar Hukumar Orsu a Jihar Imo.

Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce, “Dakarun sun tada maɓuyar IPOB/ESN kimanin guda 50 a yankin, ciki har da babbar cibiyar ‘yan ta’addan.”

Ya ƙara da cewa, “Jami’an sun kuma tarwatsa maɓuyarsu ta Buteuzor haɗa da kayayyakin gudanar da harkokinsu.

“Tsegerun sun ɓoye ne a wani tantani wanda ke hana iya bin diddinsu a inda suke.

“Tsaunin da suke ɓoye ɗin na da wadatacciyar wutar lantarki wadda duka sansanoninsu da ke yanke ke amfana da ita,” in ji shi.

Kazalika, jami’in ya ce baya ga kashe tsegeru guda 20, jami’ansu sun kuma ƙwace tarin makamai daban-daban daga hannunsu.