Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da ƙudurin dokar mafi ƙarancin albashi ga majalisar wakilai domin tantancewa tare da amincewa da shi.
An karanta wasiƙar Tinubu a zauren majalisar a yau Talata, inda ya tanadi sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa da kuma tsarin doka na aiwatar da albashin idan aka amince da shi.
A cikin wasiƙar, shugaban ya buƙaci ‘yan majalisar da su gaggauta amincewa da ƙudurin dokar mafi ƙarancin albashi domin tabbatar da aiwatar da shi cikin gaggawa domin amfanin ma’aikatan Najeriya.
Tinubu ya kuma nemi kwaskwarima ga dokar ‘yan sandan Nijeriya kamar yadda sashe na 58 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa gyara ya bada dama.
