‘Yan sandan Kano sun kama fursunan da ya tsere daga kurkukun Kuje, wanda ya kitsa kashe janar na soja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rundunar ‘Yan sanda ta yi nasarar kama wanda aka zarge shi da kitsa kisan marigayi Burgediya Janar Harold Udokwere, mai suna Hashiru Baku wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere daga kurkukun Kuje a kwanakin baya.

Jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito yadda ƴan bindiga suka shiga gidan janar Harold tare da kashe shi a unguwar rukunin gidajen Sunshine da ke Abuja a ranar 21 ga watan Yuni, inda Ƴan sanda ƙarƙashin kwamishinan rundunar Abuja, Bennet Igweh su ka kama waɗanda ake zargi kwana biyu bayan aukuwar lamarin.

A lokacin da aka gurfanar da ƴan bindigar, kwamishinan ya ce waɗanda su ka tsere daga cikin su, sun gudu da ƙaramar bindigar mamacin.

Kwamishinan ya kuma bayyana sunayen waɗanda ake zargin kamar haka; Ibrahim Rabi’u, Nafi’u Jamil, Aliyu Abdullahi da Mohammed Nuhu waɗanda dukkan su mazaunan unguwar Apo ne a Abuja.

Ya ƙara da cewa, an gano wukar da ƴan bindigar suka yi amfani da ita yayin fashin da kuma wayar mamacin a yayin farauto su.

Kazalika, ya ce suna cigaba da ƙoƙari wajen ganin an kamo sauran mutane biyun da su ka tsere tare da ƙwato ƙaramar bindigar mamacin daga gare su.

A yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin, Igweh ya ce an kama baku ne a jihar Kano a lokacin da ya ke shirin ficewa daga ƙasar.

By Babaji