
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Jami’ar Abuja ɓangaren ƙungiyar malaman jami’o’i ta sanar da dakatar da yajin aikin da aka ɗauki tsawon kwanaki 82 ana yi inda ta ce nan da nan za a dawo bakin aiki.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Sylvanus Ugo ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai bayan kammala wani zama na ƙungiyar a Abuja inda ASUU tare da majalisar zartarwar Jami’ar su ka tattauna yayin da majalisar ta yi alƙawarin yin duba ga buƙatunsu tare da samar musu da mafita a kan su.
A ranar biyu ga watan Mayu, 2024 ne aka shiga yajin aikin sakamakon karya wasu dokoki a Jami’ar ciki har da; lamuran bada muƙamai, cigaba ga mambobin ƙungiyar, tallata ɗaukar Mataimankin shugaban Jami’ar a lokacin Farfesa Abdulrasheed Na’Allah da kuma ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba.
Dakta Ugo ya ce, majalisar tare da ƙungiyar sun amince da rushe tsarin tallar gami da samar da sabon tsari da ke ɗauke da bin halastattun hanyoyi.
