
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta shiga tattaunawa kan taƙaddamar da ke tsakanin hukumar man fetur ta NMDPRA da sabon matatar Ɗangote wanda ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya jagoranta wanda Alhaji Aliko Ɗangote da shugabannin NMDPRA suka halarta.
An shirya zaman ne da nufin wanzar da haɗin kan ɓangarorin biyu da kuma warware ɓoyayyun matsalolin da ka iya shafar ayyukan matatar wanda ake tsammanin hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen dogaro da dangogin mai daga ƙasashen waje da Nijeriya ke yi.
Wata takarda da mai bai wa ƙaramin ministan shawara kan yaɗa labaru, Nneamaka Okafor, ya fitar, ta jinjina wa ministan kan ƙoƙarinsa na shiga batun a lokacin da ya dace domin samar da sulhu tare da toshe kafofin da matsaloli ka iya shiga tsakanin ɓangarorin biyu ko a nan gaba.
Ministan ya kuma jaddada muhimmancin samun haɗin kan masu-ruwa-da-tsaki wajen tafiyar da ɓangarorin albarkatun mai da na gas wanda jigo ne a ɓangaren haɓakar tattalin arziƙin Nijeriya.
Taƙaddamar ta kai matakin da shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed ke zargin matatar Ɗangote da samar da man fetur mara nagarta inda matakin sinadarin man ‘diesel’ ɗinta ya haura daga 650 zuwa 1,200 wanda ya fi wanda ake shigowa da shi daga waje.
Sai dai Ɗangote ya musa hakan, yana mai cewa 87.6 ne matakin sinadarin wanda a watan Maris, 2024 NMDPRA ta naɗa injiniyoyi 15 domin sanya ido kan gudanar ayyukan ɗakin tace man a matatar.
Kazalika, majalisar wakilai ta yi kira gare su da su sulhunta matsalolin dake tsakaninsu, don kada su sanya masu hannun jari daga ƙasashen waje su guji hulɗa da su. NMDPRA ta na jiran sabon rahoto daga matatar domin tabbatar da matakin sinadarin wanda ake tsammanin sa a ranar Litinin.
