
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya cire Wale Edun a matsayin ministan kuɗi a wani yunƙuri na yi wa gwamnatinsa garambawul, lamarin da kuma ya shafi Ma’aikatar Gine-gine da Raya Birane.
Haka kuma, Shugaban ƙasar ya tsige Umar Ɗangiwa a matsayin ministan Ma’aikatar Gine-ginen.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar, inda ya tabbatar da sauye-sauye a manyan ma’aikatun tattalin Nijeriya.
A cewar takardar, an umarci Edun ya miƙa ragamar jagorancin Ma’aikatar Kuɗi da Harkokin ga Mista Taiwo Oyedele, wanda a yanzun zai fara aiki a muƙamin.
Oyedele, wanda a baya shi ne ƙaramin ministan kuɗi, zai karɓi jagorancin ma’aikatar a babban matakin ba tare da wani jinkiri ba.
A wani ɓangare kuwa, an fitar da sunan Dakta Muttaqha Rabe Darma a matsayin wanda ake sa ran zai zama sabon ministan gine-gine da ci-gaban birane.
Tuni dai aka umarci Ɗangiwa da ya miƙa ragamar jagorancin ma’aikatar ga ƙaramin ministan kafin kammala aikin garambawul ɗin.
Kazalika, an umarci waɗanda lamarin ya shafa da su kammala miƙa lamuran muƙaman daga yanzu zuwa ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.
